Connect with us

Wasanni

Inter na bukatar maki 16 domin ta lashe Serie A na bana

Published

on

Inter Milan ta yi nasarar cin Cagliari 1-0 a wasan mako na 30 a gasar Serie A da suka fafata ranar Lahadi.

Tsohon dan wasan Manchester United, Matteo Darmian shi ne ya ci kwallon tilo, saura minti 13 a tashi daga wasan.

Da wannan sakamakon Inter ta yi nasara a wasa 11 a jere a gasar ta Italiya ta kuma ci gaba da zama ta daya a kan teburi da tazarar maki 11.

Inter wadda Antonio Conte ke jan ragama na bukatar maki 16 nan gaba daga sauran karawa takwas da ta rage a wasannin Serie A ta bana.

Rabon da Inter Milan ta lashe kofin gasar Italiya tun kakar 2009/10.

AC milan ce ke mataki na biyu a kan teburin Serie A mai maki 63 da tazarar maki daya tsakaninta da Juventus wadda ta doke Genoa 3-1 a wasan mako na 30 ranar Lahadi.

Juventus wadda take ta uku a teburi da tazarar maki 12 tsakaninta da Inter, ita ce mai rike da kofin Serie A, kuma na tara da ta lashe a jere.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Wasanni

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Oblak, Konate, Kabak, Vestergaard, Icardi, Johnstone

Published

on

By

Manchester United na ci gaba da sha’awar daukar golan Atletico Madrid Jan Oblak, mai shekara 28, kuma dan wasan na Slovenia zai samu damar sauya kungiya. (90min)

A gefe daya, kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce har yanzu dan wasan Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 34, ba shi da tabbacin ci gaba da zama a kungiyar a kakar wasa mai zuwa. (Manchester Evening News)

Liverpool za ta iya sayen dan wasan RB Leipzig da ke buga gasar ‘yan kasa da shekara 21 a Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 21, a kan kasa da euro 40m kamar yadda aka sanar a farkon shekarar nan. (Bild journalist Christian Falk)

Southampton za ta “yi dukkan mai yiwuwa” domin rike dan wasan Denmark Jannik Vestergaard, mai shekara 28, a cewar kocin kungiyar Ralph Hasenhuttl a yayin da wasu rahotanni ke cewa Tottenhamna zawarcinsa(Daily Echo)

Continue Reading

Wasanni

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Ronaldo, Kane, Pedri, Suarez, Neves, Mbappe da Ibrahimovic

Published

on

By

Dan wasan gaban Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, zai iya tafiya Paris St-Germain idan dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, ya zabi tafiya Real Madrid. (Tuttosport, via Mirror)

Kazalika Real Madrid na kallon kanta a matsayin wacce ke kan gaba a yunkurin daukar Mbappe a bazara. (AS)

Liverpool ta bayyana aniyarta ta daukar dan wasan tsakiyar Barcelona Pedri, abin da ya sa Barca ta nemi sabunta kwangilar dan wasan na Sifaniya mai shekara 18 da karin kudi da ya kai kusan £350m. (Sunday Mirror)

Ana hasasen cewa dan wasan gaban Atletico Madrid Luis Suarez zai koma Liverpool, shekara bakwai bayan dan kasar taUruguay ya bar kungiyar. Kazalika ana rade-radin cewa zai tafi kungiyar Inter Miami ta David Beckham. (Todofichajes, via Sun on Sunday)

Dan wasan gaban Ingila Harry Kane, mai shekara 27, zai matsa lamba domin ganin ya bar Tottenham a bazara idan kungiyar ta gaza samun gurbin zuwa gasar Zakarun Turai ta kakar wasa mai zuwa. (Athletic – subscription required)

Continue Reading

Trending

Copyright © Martaba FM Funtua 2021. All Rights Reserved | Design by Sharfadi Technology