Connect with us

Noma da Kiwo

Lafiya Jari: Cutar Zaizayar baki

Published

on

Alkalumman hukumar lafiya ta duniya WHO sun bayyana cewar akalla mutum dubu dari da arbai’n ne ke kamuwa da wannan cuta ta zaizayar baki kowa ce shekara.

Kokarin da duniya keyi na yakar cutar da kuma gammayyar likitocin nagari na kowa MSF da likitocin Assibitin ta Noma dake jihar sakkwato yasa ana samun fadakarwa a yankunan karkara ciki da wajen Najeriya dangane da cutar wacce ke wanzuwa a dalilin wasu matsalolin na kiwon lafiya, sun hada a samun karancin abinci da ke gina jiki. A Najeriya da Nijar akwa cibiyoyi a Kasar Jamus ta girka domin yaki da cutar.Wannan shi ne batun da shirin kiwon lafiya na(06-04-21) ya duba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Noma da Kiwo

Sabon salon rikicin makiyaya a Najeriya

Published

on

By

A wani abu da ke zaman alamun sauyin salo a rikicin makiyaya da manoma a Najeriya, ana ka-ce-na-ce tsakanin gwamnatin jihar Ondo da ta nemi makiyaya su bar dazuzzukan jiharta da kuma gwamnatin kasar da ke fadin ba hali.

Kama daga sashen arewacin kasar zuwa na Kudu dai, batu na satar al’umma da karbe kudin fansa na zaman kan gaba cikin jerin rashin tsaron da ke tashi da lafawa. To sai dai kuma wata sanarwar mahukuntan jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin kasar a kan Fulani makiyaya, na shirin bude sabon babi a cikin rikicin noma da kiwon da ke shirin rikidewa ya zuwa na siyasa. Wannan ne dai karo na farko da wata jiha cikin Tarayyar Najeriyar ke fitowa karara, tare da umartar Fulanin da ke sana’ar kiwo a dazukan jihar su tattara su bar cikinta cikin wa’adin mako daya tilo.

Karin Bayani:Najeriya: Kokarin shawo kan rikicin filin noma

To sai dai kuma tuni umarnin ya tayar da hankali cikin Najeriyar, inda gwamnatin kasar ke fadin ba a isa ba. Abujar dai ta ce jihar ta  Ondo koma duk wani sashe na kasar, ba shi da ikon korar duk wani dan kasar da ke bukatar ya zauna cikin wani sashe, a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakakin fadar gwamnatin Najeriyar. Koma ya zuwa ina idon na gwamnatin ke shirin ya kai da nufin bayar da kariya ga dubbai na Fulani makiyayan da ke fuskantar barazana mai girma dai, matakin jihar ta Ondo na dada nuna alamun rikidewar rashin tsaron kasar ya zuwa na siyasa mai muni.

Continue Reading

Noma da Kiwo

Najeriya da rikicin Afirka a jaridun Jamus

Published

on

By

Jaridar Die Tageszeitung ta rubuta sharhi mai taken” Shell zai biya kudin diyya saboda gurbata muhalli” a Najeriya bayan hukunci da kotu ta yanke wa kamafanin mai na Shell, hukuncin da ake wa kallon ya na da illoli.

Wata kotu da ke da matsugunni a birnin The Hague na kasar Netherlands ta yanke wa kamafanin albarkatun mai na Shell hukuncin biyan kudaden diyya ga wasu manoman yankin Niger Delta da ke kudancin Nageriya, hukuncin da ake wa kallon ya na da illoli.

Jaridar Die Tageszeitung ta ce an samu katafaren kamfanin na Royal Dutch Shell da laifin gurbata muhalli a Najeriya. A ranar Jumma’ar da ta gabata ne dai aka yanke wannan hukuncin bayan daukaka kara da manoman suka yi bayan hukuncin farko da ba su amince da shi ba. Kamfanin a daya bangaren ya dora alhakin lalata muhallin kan masu fasa bututun mai a yankin Niger Delta. Hukuncin kotun na birnin The Hague na nuni da cewar kauyuka biyu ne za a biya mukudan kudade biyo bayan bata musu filayen noma, duk da cewar ba a sanar da yawan kudin da za a  biya ba.

Nigeria Öl im Niger Delta Frau mit EssenManoman yankin Niger Delta sun yi nasarar a kan Shell

Wata kungiyar fafukar kare muhalli da wasu manoma hudu ne dai suka shigar da karar kamfanin na Shell a gaban kotu a shekara ta 2008, saboda gurbata filayensu da mai da kamfanin ya yi. Duk da cewar kotun kai tsaye ba ta sami kamfanin da laifin ba, ta ce hakkin kula da al’umma da abubuwan da ke gudana a kewayensu ya rataya a wuyan shell. Hukuncin dai ya samu martanin farin cikin daga bangaren masu shigar da karar.

Continue Reading

Noma da Kiwo

Rikicin Fulani da Makomar kiwo a Najeriya

Published

on

By

A yayin da ake ci gaba da neman mafitar rikicin makiyaya da manoma, hankali yana ta karkata a zuciyar mahukuntan Najeriya na kare tsarin kiwon gargajiyar shekaru aru-aru a kasar.

Ra’ayi dai daga dukkan alamu yana zuwa daya, a tsakanin shugabanin a Najeriyar, walau a sashen kudancin ko na arewaci, game da kare batun kiwon dabbobbi na al’ada. Wani taron gwamnonin arewacin kasar dai, ya bi sahun ‘yan uwansa da ke kudanci wajen yanke hukuncin cewar kai kawon shanu da Fulanin ba zai  dore a cikinNajeriyar ba, kasar da ke kallon karuwar tayar da hankali sakamakon rikicin makiyaya da manoma da kuma siyasar da ta mamaye shi a yanzu.

Karin Bayani: Fulani makiyaya cikin fargaba

Gwamnonin dai sun ce dole masu sana’ar kiwon su rungumi ajiye shanun wuri guda, domin kai karshen gwagwarmaya ta mallakar filayen noma ko kuma burtulai da ta rikide zuwa barazanar tsaron kasar mai girma. Tun kafin yanzu dai, jihohi da daman gaske sun kai ga ware daruruwan miliyoyin Nairori da sunan sake tsugunar da masu sana’ar kiwon da ke zaman masu sana’a daya tilo da babu tallafin gwamnati cikin sana’ar tasu.

Continue Reading

Trending

Copyright © Martaba FM Funtua 2021. All Rights Reserved | Design by Sharfadi Technology