Connect with us

Labarai

Sakamakon zaɓe nake jira – Idriss Deby

Published

on

Shugaban Chadi Idriss ya yi watsi da zargin danne ƴan dawa da kuma kiran ƙauracewa zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a yau Lahadi.

Shugaba Deby bayan kaɗa ƙuri’arsa tare da matarsa Hinda Deby ya zanta da manema labarai inda ya ce “ina jiran sakamakon hukuncin da masu zaɓe suka yanke.”

Ana na sa ran Idriss Deby zai lashe zaɓen a wa’adi na shida.

An zargi Shugaba Deby wanda ya kwace mulki a wani juyin mulki da aka yi a 1990 da muzgunawa yan adawa gabanin zaben.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch na cikin ƙungiyoyin da suka zargi shugaban ƙuntatawa yan hamayya da masu zanga-zanga.

Kungiyar ta ce an yi amfani da karfi a zanga-zangar kin jinin gwamnatin da aka yi a kwanakin baya.

Daga cikin ƴan takarar da ke fafatawa da Deby sun haɗa da tsohon Firaminista Albert Pahimi Padacke, yayin da sauran ƴan adawa suka ƙauracewa zaɓen ciki har da babban mai hamayya da shi a zaɓen 2016 Saleh Kebzabo.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

An yi zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyyar Benin

Published

on

By

Al’ummar Benin sun kaɗa kuri’ar zaɓen zaben shugaban kasa a ranar Lahadi

Shugaba mai ci Patrice Talon shi ne ake sa ran zai sake lashe zaben a wa’adi na biyu.

Ƴan na zarginsa da shirya magudi a zaben ta hanyar dakatar da manyan masu adawa da shi tsayawa takara.

An yi ta zanga-zanga gabanin ranar zaben a yankin arewacin ƙasar.

Rahotanni sun ce an kashe mutum biyu a lokacin da sojoji suka tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Savey.

Continue Reading

Labarai

Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya biyu a Damasak

Published

on

By

Rahotanni sun ce wasu ƴan bindiga da ake tunanin ƴan Boko Haram ne sun kashe sojojin Najeriya biyu a jihar Borno yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Bayanai sun ce an kashe sojojin ne a wani kwantan ɓauna da aka yi masu yayin da suke farautar mai taimakawa Boko Haram da bayanai.

Jaridar PRNigeria da ke da kusanci da jami’an tsaron Najeriya ta ce ƴan bindigar sun kai harin ne a garin Damasak a ranar Asabar.

Sun kuma kwashi kayayyakin jin ƙai tare da kashe wasu mutane biyu. Sun kuma cinna wuta a gidan babban jami’in ƴan sanda na yankin wuta da kuma gidan basarake.

Kafar ta ce an kashe ƴan Boko Haram da ISWAP da dama a harin sama da aka kai masu

Continue Reading

Labarai

Iran ta ce harin ta’addanci aka kai wa cibiyar nukiliyarta

Published

on

By

Hukumar da ke kula da makamashin Nukiliya a Iran ta tabbatar da cewa an harba wani makami a tasharta da ke Natanz.

Gwamnatin Tehran ta ce babu tantama harin ta’addanci ne aka kai mata.

Harin na zuwa ne kwana daya bayan da shugaba Rouhani ya kaddamar da sabon shirin Iran na ci gaba da tara sinadarin Uranium wanda aka nuna kai tsaye ta gidajen talabijin.

Rahotanni sun ce babu wanda harin ya jikkata, kuma tuni hukumomi a Iran din suka zargi Israila da kai shi.

Continue Reading

Trending

Copyright © Martaba FM Funtua 2021. All Rights Reserved | Design by Sharfadi Technology