Connect with us

Tarihi da Al'adu

Zaben fidda gwani tsakanin ‘yan takara

Published

on

A Jamhuriyar Nijar al’umma na ci gaba da kada kuri’a a zaben shugaban kasa zagaye na biyu don tantance wanda zai jagoranci kasar na tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Da misalin karfe takwas na safe ne akasarin rumfunan zabe suka bude a birnin Yamai, rumfar zabe mai lamba 001 inda shugaban kasa da sauran mambobin gwamnati da manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa ke kada kuri’ar tasu. Bayan kada kuri’arsa, shugaban kasa Alhaji Mahamadou Issoufou ya bayyana gamsuwarsa da wannan rana wacce ya bayyana a matsayin ta tarihi yana mai cewa “Ina mai farin cikin kasancewa zababben shugaban kasa na farko a tarihin kasar nan da ke shirin mika mulki ga wani zababben shugaban kasa, abun alfahari ne ga siyasar kasar nan.”

Niger | Präsidentschaftswahlen in Zinder | Kandidat Mahamane OusmaneMahamane Ousmane dan takarar shugaban Nijar

Dan takarar jam’iyyar adawa Alhaji Mahamane Ousmane ya gudanar da nashi zabe ne a mahaifarsa ta Damagaram, a yayin da dan takarar jam’iyya mai mulki Malam Bazoum Mohamed wanda shi ma dan jihar ta Damagaram ne ya gudanar da na shi zabe a birnin Yamai. Jama’a dai na yanzu ci gaba da yin tururuwa zuwa runfunan zabe domin kada kuri’ar tasu a birnin Yamai da sauran yankunan kasar duk da jinkirin da aka samu a wasu sassan Nijar na rashin bude rumfunan zabe da wuri.

Hukumar zaben kasar ta Nijar ta ce kawo yanzu babu wata matsala a cikin tafiyar da zaben, sai dai ta ce ta bankado wata manakisa ta neman shirya magudi. Ya zuwa yanzu dai zaben na gudana a cikin tsanaki a cikin birnin na Yamai inda aka jibge tarin jami’an tsaro a bakin rumfunan zabe da a wasu manyan titunan birnin Yamai don ganin zaben ya wakana a cikin kwanciyar hankali da lumana.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Tarihi da Al'adu

Paparoma Francis ya suka Iraki

Published

on

By

Mabiya addinin Kirista a Iraki da ke zama tsiraru cikin al’umma na rayuwa  cikin yanayi na tsananci da fuskantar wariya, kuma su na shakkar ko rangadin kwanaki hudu na Paparoma Francis zai kawo wani sauyi.

Shugaban darikar Roman Katolika Paparoma Francis ya fara ziyarar kwanaki hudu mai taken ” dukkanmu ‘yan uwan juna ne” a Iraki. Ziyarar da ke zama irinta ta  farko a tarihi a bangaren wani Paparoma a kasar ta Iraki. Shugaban roman katolikan dai zai halarci addu’o’i a majami’un da ke babban birnin kasar, da filin wasan kwallon kafa na birnin Irbil da ke arewaci. Kazalika zai gana da manya limaman musulunci a birnin Najaf da ke kudanci, kafin ya shige zuwa birnin Mosul da jirgi kirar saukar ungulu.

Shugabannin majami’u dai na bayyana barazanar karewa tsakanin al’ummar musulmi masu rinjayen kasar, inda suka yi hasashen makamancin wannan matsalar a tsakanin kananan al’ummomin kirista kamar yadda lamarin ya kasance da al’ummar Yahudawan Irakin da a baya suke bunkasa. Wasu na cewar a yanzu, kasa da Yahudawa 10 kawai ke zaune a birnin Bagadaza.

Continue Reading

Tarihi da Al'adu

Ranar tunawa da cinikin bayi ta duniya

Published

on

By

Potugal na zaman kasar Turai ta farko da ta fara mulkin mallaka a duniya, hakan ya sa ta zama kasa ta farko da ta fara cinikin bayi tsakanin Afirka da kasashen Yamma.

A yayin da duniya ke bikin tunawa da zamanin cinikin bayi, yawancin ‘yan Potugal wadanda ke da tsatson Afirka na ci gaba da jaddada bukatar yin nazarin wannan mummunan babi a tarihi. 25 ga watan Maris na kowace shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da halin da wani rukuni na mutane suka tsinci kansu a ciki na bauta bayan an yi cinikinsu a matsayin bayi. Ana daukar Potugal kasar Turai ta farko da ta yi mulkin mallaka a duniya, kana jagora a harkar cinikin bayi na kasa da kasa. Ana alakanta halin kyama da nuna wariya da bakaken fata suka tsinci kansu a ciki a yanzu da tarihin yadda aka yi ta jigilar ‘yan Afirka a matsayin bayi ta Tekun Bahar Rum a karni na 15.

Karin Bayani: Har yanzu ana bauta a Mauritaniya

Shugabar kungiyar wadanda suke da asali da Afrika da ke da tsatso da kasar Guinea Bissau a birnin Lisbon, Evalina Dias ta koka da yadda Potugal da danne batun cinikin bayin: “Tsawon lokaci Portugal ta yi watsi da tarihin mulkin mallaka da bukatar mayar da bayin da suka fito daga Afirka gida. Al’ummar Potugal kan yi bukukuwa na harkokin da suka shafi wadannan rukuni na mutane, amma a fakaice sukan yi kokarin boye wannan bakin tarihi a rayuwarsu, wato fataucin bayi ta Tekun Bahar Rum.”

Continue Reading

Trending

Copyright © Martaba FM Funtua 2021. All Rights Reserved | Design by Sharfadi Technology